in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar wasan kwallon kafan Rasha ta yi tur da rikicin da ya barke a UEFA Euro 2016
2016-06-16 15:11:27 cri
Kungiyar wasan kwallon kafa ta Rasha ta yi Allah wadai da tarzomar data barke a daren Asabar data gabata a birnin Marseille na kasar Faransa a lokacin gudanar da wasa tsakanin England da Rasha a wasannin UEFA Euro 2016.

Cikin wata sanarwa da jami'an hukumar kwallon kafan suka fitar a shafin sadarwa na zamani, kungiyar 'yan wasan kwallon kafan Rasha tayi tur da matakin da 'yan wasan kwallon kafan Rashar suka dauka na haddasa tashin hankali a lokacin da ake tsaka da buga wasannin.

Dama dai tunda farko, sai da hukumar wasan kwallon kafar ta Rasha ta yi gargadi ga 'yan wasan, dasu kasance masu da'a da kuma bindoka da oda tare da nuna karamci ga abakan karawar su tun gabannin fara wasannin a kasar Faransa.

Ta kara da cewar, hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta kasa da kasa tana bibiyar yadda wasannin ke gudana, sannan kungiyar tayi gargadin cewar hukumar zata ladaftar da duk wanda aka samu da hannu wajen nuna rashin da'a.

Hukumar shirya wasanin ta UEFA ta tanadin matakan ladaftarwa tun a lokacin data hada tawagar yan wasan na UEFA EURO 2016 da suka hada da wasannin tsakanin England da Rasha, da Albania da Switzerland, sai kuma Turkiyya da Croatia.

UEFA ta zargi Rasha da haddasa rikicin, musamman wajen yin hargowa, da yin wasan wuta, harma da harbe harbe a filin wasan.

Babban kwamitin na UEFA, ya gargadi England da Rasha cewar ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ladaftar da duk wanda aka gano yana da hannu wajen haddasa rikicin, daga cikin hukuncin har da haramtawa kungiyar wasan shiga wasannin a nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China