Mataimakin babban jagoran kungiyar Ed Woodward ne ke jagorantar tattaunawa da wakilan Ibrahimovic, ana kuma hasashen cewa dan wasan mai shekaru 34 a duniya, zai fara takawa Man United kwallo kafin gasar kasashen turai dake tafe nan gaba cikin wannan shekara ta 2016.
A baya dai Ibrahimovic ya taka leda a kungiyoyin Malmo, da Ajax Amsterdam, da Juventus, da Inter Milan, da Barcelona da kuma AC Milan. Yanzu kuma kwantiragin sa na daf da kammala a kungiyar PSG. Ya kuma dauki kofuna tare da kungiyoyi daban daban da ya bugawa wasa, ciki hadda kofin Premier na Ingila, da kofin zakarun kulaflikan Swiden, da Serie A na Italiya, da La Liga ta Sifaniya, da kuma Ligue 1 na kasar Faransa.
A wasannin share fagen gasar nahiyar turai kuwa, Ibrahimovic ya zura kwallaye 11 cikin 19 da Sweden ta ci, wanda hakan ya baiwa kungiyar ta sa ta Sweden gurbi a gasar da za a buga a kasar Faransa.(Saminu Alhassan)