in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta tashi kunne doki da Swaziland a wasannin Cosafa 2016
2016-06-16 15:10:25 cri
Zimbabwe da Swaziland sun tashi da ci 2 da 2 a wasan da suka buga a kasar Namibiya a ranar Asabar din data gabata a rukunin A a gasar wasanni ta Cosafa na 2016.

Dan wasan Swaziland Felix Badenhorst shine ya zara dukannin kwallayen biyu.

Badenhorst ya zara kwallo ta farko ne a wani bugun gaba da gaba mintuna 15 da fara wasan wanda a aka gudanar a filin wasa na Sam Nujoma.

Ya zara kwallo ta biyu mintuna 65 da fara wasan a yayin wani bugun daga kai sai mai tsaron gida yayin da wani dan kasar Zimbabwe Danny Phiri ya taba kwallon da hannu.

A bangare guda 'yan wasan Zimbabwe Elisha Muroiwa da Obadiah Tarumbwa ne suka samu nasarar zara kwallayen biyu.

Tarumbwa ya zara kwallon ne 'yan mintuna kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, yayin da Muroiwa ya zara kwallo ta biyu mintuna 10 kafin kammala wasan.

Mai horas da 'yan wasan na Swaziland, Harries Bulunga, yace 'yan wasan sun taka rawa mai kyau daga farkon fara wasan zuwa karshe, sai dai basu yi amfani da irin damammakin da suka samu ba a wasan.

Kalisto Pasuwa, shine kociyan Zimbabwen yace ya gamsu da ikirarin da Bulunga yayi na cewa 'yan wasan na Swaziland sun zubar da damammaki masu yawa wadanda zasu iya kaisu ga yin nasara a lokacin wasan.

Pasuwa yace yana fatar 'yan wasan nasa zasu dauki darrusa a lokacin gudanar da wasannin su a nan gaba.

Wasan tsakanin Zimbabwe da Swaziland yayi matukar armashi, kuma ya samu halartar daruruwan 'yan kallo wadanda suka dinga gudanar da raye raye a lokacin da wani fitaccen mawaki dan namibiya Adora Kisting yake rera wakoki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China