Sakatare janar na kungiyar zirga-zirgar jiragen saman ta Afrika AFRAA Elijah Chingosho ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Alhamis din nan a Nairobi cewar, kasashen Afirka wadanda adadinsu ya kai kashi 85 cikin 100 sun amince da zirga zirgar jiragen saman na kasashen Afrika a sararin samaniyar su.
Kasashen da suka amince da aiwatar da yarjejeniyar Yamoussoukro na ba da dama ga sauran kamfanonin zirga-zirgar jiragen saman Afirka da su bi a sararin samaniyarsu sun hada da Najeriya, da Masar, da Habasha, da Morocco da Kenya. Sauran su ne Afrika ta kudu, da Rwanda da kuma Zimbabwe.
Idan dai har aka amince da jiragen saman na kasasshen Afrika su gudanar da zirga zirgar a sararin samaniyar, matakin zai bada dama ga jiragen saman yin zirga zirgar tsakanin kasashen na Afrika a kowane lokaci ba tare da fuskantar wata turjiya ba.
Chingosho, ya kara da cewar idan har hukumomin kula da sufurin jiragen saman kasashen Afirka suka amince da wannan matakin, za'a samu ninkin ba ninkiya na zirga zirgar jiragen sama a nahiyar cikin shekaru biyar masu zuwa. (Ahmad Fagam)