A jiya Alhamis ne, wani jirgin sama na kamfanin zirga-zirgar jiragen saman kasar Masar wanda ya tashi daga birnin Paris na kasar Faransa zuwa Alkahira na kasar Masar ya bace a yankin tekun Bahar Rum. Ministan harkokin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Masar Sherif Fathy ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar kan batun bacewar jirgin sama mai lamba MS804 na Masar a wani ginin dake dab da filin jiragen saman birnin Alkahira a yammacin jiya cewa, yanzu ana gudanar da bincike don gano musabbabin bacewar jirgin saman. Koda yake mai yiwuwa ne jirgin saman ya fadi, amma kafin a gano tarkacen jirgin saman, yana da kyau a yi amfani da kalmar 'bace' maimakon 'fadi'.
A nasa bangare, shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana a tsakar ranar 19 ga watan a birnin Paris cewa, yanzu ba a tabbatar da dalilin faruwar hadarin ba. (Zainab)