in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu 'yan Burundi na tserewa daga kasar in ji UNHCR
2016-04-28 10:11:54 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ko UNHCR, ta ce cikin shekara guda, 'yan Burundi 260,000 ne suka kauracewa kasar domin tsira daga tashe tashen hankula dake ci gaba da kazanta.

Wata sanarwar da hukumar ta UNHRC ta fitar, ta ce akwai yiwuwar karin al'ummar kasar za su fice zuwa makwaftan kasashen irin su Tanzania, muddin ba a gaggauta daukar matakan warware rikicin siyasar dake addabar kasar ba.

Tanzania dai na karbar tarin masu neman mafaka a kullum daga kasar ta Burundi, wadanda yawan su ya tasar ma mutum 130 a ko wace rana. Kana mafi yawancin 'yan gudun hijirar da suka haura mutum 71,000, na zaune ne cinkushe a sansanin 'yan gudun hijira na Nyarugusu, dake yankin Kigoma.

Sanarwar ta kara da cewa, da yawa daga 'yan gudun hijirar na bayyana karuwar laifukan cin zarafin al'umma, da azabtarwa, da fyade, da tsare mutane babu dalili, tare da tirsasa shigar da al'umma cikin rundunonin yaki a kasar ta Burundi.

A yunkurin ta na shawo kan yanayin da ake ciki, hukumar 'yan gudun hijirar ta ce tana daukar matakan yiwa a kalla mutane 330,000 tanajin kayayyakin jin kai nan da karshen wannan shekara.

A daya hannun kuma ta bukaci kasashen duniya da su samar da karin tallafi, domin rage kalubalen da ake fuskanta, tare da bunkasa shirin shiga tsakani a Burundi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China