Babban mai shari'a na kasar Valentin Bagorikunda, ya fada a Juma'ar data gabata cewa, ana cigaba da gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ake zarginsu da hannun a wannan danyen aiki.
Marigayi birgediya janar Athanase Kararuza, shi ne babban mai bada shawara ta fuskar tsaro a ofishin mataimakin shugaban kasar, kuma an harbe shi ne a daidai lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki da safiyar ranar Litinin a babbban birnin kasar Bujumbura.
Kuma a lokacin yana cikin motarsa inda aka hallaka shi tare da matarsa da mai tsaron lafiyarsa nan take, sannan 'yarsa ta samu munanan raunukuna a lokacin harin, sai dai ita ma daga bisani ta rasu a ranar Alhamis din data gabata.
Bagorikunda ya ce, ana cigaba da shari'a ga wasu da ake zargi da kashe wasu manyan jami'an sojojin kasar a 'yan watannin da suka gabata.(Ahmad)