in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci daukar matakan dakile masu cinikayyar dabbobi da tsirrai ba bisa ka'ida ba
2016-06-06 10:23:23 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya gabatar da jawabin ranar kiyaye muhalli ta duniya a jiya Lahadi 5 ga watan nan, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su dauki matakai na yaki da cinikayyar sassan dabbobi da tsirrai ba bisa ka'ida ba.

A cikin jawabin na sa, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, abin da ya fi jawo hankalin duniya a wannan rana ta kiyaye muhalli ta duniya ta bana shi ne, maida hankali ga cinikayyar dabobbi da tsirrai ba tare da izini ba.

Ya ce ya kamata a maida hankali ga wannan batu, duba da cewa wasu kamfanoni da mutane na gurbata yanayi domin samun riba, kana wasu na mu'amala da kungiyoyi masu aikata manyan laifuffuka, wadanda hakan ke haifar da baraka ga kasashen duniya a fannin samuwar yanayin da ake bukata.

Ban Ki-moon ya bayyana cewa, a wannan rana ta kiyaye muhalli ta duniya, yana kalubalantar gwamnatocin kasa da kasa, da jama'arsu, da su maida hankali wajen daukar matakai na tabbatar da wanzuwar albarkatun halittu, domin amfanin 'yan baya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China