Magoya da masu sukar JCPOA suna wuce gona da iri, kan alfanusa da kuma bakin iyakarsa, in ji mista Khamenei, tare da kara cewa yana kunshe da wasu kura-kurai da dan rauni da abokin gaba ya yi amfani da wata muguwar manufa.
Wancen bangare ya dauki niyyar soke takunkumi kan Iran da kawo karshen hana hada-hadar kudi tsakanin bankunan Iran da sauran kasashen duniya, amma bai aiwatar da matakan da ake magana kansu ba, in ji Ali Khamenei.
"Amurkawa ba su cika yawancin muhimman alkawuransu ba, a yayin da muka cimma matakan farko, dakatar da tace sanadarin nukuliya zuwa kashi 20 cikin 100 da kuma rufe yankin tace sanadarin nukuliya na Fordow da tashar nukuliya ta Arak", in ji Ali Khamenei.
Jagoran musuluncin Iran ya jaddada cewa ba za su karya shirin JCPOA ba. Amma idan wancen bangare ya nemi ya karya shi, a yayin da wasu 'yan takarar zaben shugaban kasa Amurka suke barazanar su gutsuntsuna shi, to za mu sanya wuta.
A shekarar da ta gabata ne, Iran da manyan kasashen duniya suka cimma wata yarjejeniya, da ta fara aiki a cikin watan Janairu, kan tsohon shirin nukuliya na Iran, da ake takadama kansa sosai.
Kamar yadda yarjejeniyar ta tanada, Iran ta yi watsi da yawancin shirinta na nukiliya sannan a soke mata rabin takunkumi a bangarorinta na makamashi da kudi. (Maman Ada)