A wata sanarwar da aka fitar a Litinin din data gabata, shugabannin biyu sun cimma matsayar ne bayan tattaunawar sirrin da suka gudanar a matsayin wani bangare na ziyayar aiki ta kwanaki biyu da shugaba Mahama ya kai a jamhuriyar musuluci ta Iran.
Da yake zantawa da 'yan jaridu bayan kammala ganawar tasu, shugaba John Mahama, ya bayyana cewar ya zama tilas su hada gwiwa a yayin da ake fuskantar yawaitar ayyukan masu tsattsauran ra'ayi a duniya.
Ya kara da cewar, matsalar hare hare daga masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ta'adda babbar barazana ce ga duniya baki daya, kuma za'a yi nasarar magance ta ne kadai ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashe.
Mahama ya ce, matsalar masu tsattsauran ra'ayi ta shafi kasashen Afrika, misali: yanayin da ake ciki a Libya yana shafar yankunan kasashen Sahel na Afrika, ga rikicin mayakan Al-Qaeda a yankin Maghreb, da kuma na Boko Haram, dukkanin wadannan matsaloli ne dake barazana ga zaman lafiyar Afrika.
Shugaban na Ghana, ya bayyana cewar, sun tattauna muhimman batutuwa biyu da suka hada da yakar akidojin masu tsattsauran ra'ayi ta hanyar al'adu, sannnan sai amfani da dabaru irin na zamani ta hanyar hadin gwiwa don yakar ta'addanci.
Ban da haka kuma, Mahama ya yabawa Rouhani game da irin matakan da yake dauka domin yakar ta'addanci.(Ahmad Fagam)