in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta sanar da cewa Musulmai a kasar ba za su je aikin hajji a bana ba
2016-05-30 13:07:20 cri
A jiya Lahadi ne, ministan al'adu da harkoin addini na Iran, Ali Jannati ya bayyana cewa, ba zai yiwu Musulmai a kasar su je aikin hajji ba a bana.

Kamfanin dillancin labaru na jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa, a wannan rana Ali Jannati ya ba da sanarwar cewa, sabo da ba a cimma matsaya daya kan jigilar fasinjoji ta jirgin sama, da ba da izni, da ba da tabbaci ga tsaro da sauransu tsakanin bangarorin Saudiya da Iran ba, shi ya sa bana ba zai yiwu ba Musulmai a kasar Iran su je hajji a Mekka. A yau ne ake saran ma'aikatar kula da harkokin aikin hajji ta jamhuriyar Musulunci ta kasar Iran za ta sanar da al'ummar kasar dangane da wannan batu.

A watan Janairun bana ne, dangantaka tsakanin Saudiya da Iran ta tsananta, bayan da mahukunta kasar Saudiya suka kashe wani fitaccen mai bin addinin Musulunci dan darikar Shi'a. Daga watan Afrilun bana zuwa yanzu, Iran da Saudiya sun yi shawarwari da dama, amma ba su cimma wata matsaya game da batutuwan da suka shafi aikin hajji na bana ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China