Jakadan kasar Ghana dake Najeriya, Williams Awinador-Kanyirigi, ya fadi haka a birnin Abuja, lokacin da ya gana da ministan harkokin cikin gida na Najeriya, laftanar janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya.
Awinador, ya jaddada tasirin huldar dake tsakanin kasashen 2 inda ya bayyanata da cewa mai dadaddan tarihice, kuma ya jaddada bukatar karfafa ta a dukkan fannoni, musamman ma fannin tabbatar da tsaro.
Jakadan ya ambaci matsalar hare-haren da wasu makiyaya ke kaddamarwa a kan wasu manoma a Najeriya, batun da ya zama barazana ga aikin tsaro da hadin kan al'ummar kasar.
A cewarsa, Ghana ita ma tana fuskantar irin wannan matsaloli, don haka yana fata kasashen 2 za su yi musayar fasahohinsu don daidaita wannan batu.
A nasa bangaren, Dambazau ya jaddada bukatar karin hadin gwiwar kasashen 2 a fannin aikin tsaro na cikin gida.
Haka kuma ya yi kira da a kara musayar bayanai da aka samu dangane da yanayin jigilar makamai, da aikata lafuka tsakanin kasa da kasa, da fataucin mutane, da karya dokoki ta hanyar amfani da yanar gizo, da makamantansu.(Bello Wang)