A cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa, mista Ban ya nuna cewa matsayar da aka cimma an same ta ne tare da taimakon kokarin kwamitin ruwa biyu da ke sanya ido da kimantawa, har ma da abokan huldar shiyoyyi da kuma na kasa da kasa.
Shugaban MDD ya bayyana fatan ganin cewa wannan matsayar da aka cimma za ta taimakawa wajen kafa wata gwamnatin hadin kasa na wucin gadi cikin wannan kasa cikin gaggawa da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka rattabawa hannu a cikin watan Augustan shekarar 2015.
Haka kuma, ya yi kira ga dukkan abokan hulda na shiyoyyi da na kasa da kasa da su ci gaba da tallafawa ci gaban aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya. (Maman Ada)