Taron wata muhimmiyar dama ce domin babban taron ya kai ga cimma wata fahimta mai kyau kan wannan batu bisa tsarin aiki na sakatare janar dake shafar yin rigakafin kaifin kishin addini da kuma a lokacin da muke nazarin dubarar baki daya kan yaki da ta'addanci dake da shekaru goma, in ji shugaban babban taron MDD, mista Mogens Lykketoft.
Yara da matasa sun yi fama ta fuskar tashin hankali kana sosai daga kaifin kishin addini a tsawon shekarun baya bayan nan, matasa sun yi fama ta fuskar mataki mataki game da bambance bambance, tauye hakki da kuma rashin aikin yi, in ji a nasa bangare mataimakin sakatare janar na MDD, Jan Eliasson, a cikin jawabinsa.
Ya tunatar da cewa asusun MDD na karfafa zaman lafiya ya kaddamar da wani shiri zuwa ga matasa. Wannan shiri na samarwa kungiyoyin matasa wani tallafin kudi domin ba su damar kafa ayyukan kansu na karfafa zaman lafiya. (Maman Ada)