in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga kasa da kasa da su hada kai wajen tinkarar matsalar fataucin mata da yara a lokacin rikici
2016-06-03 13:16:54 cri
A jiya ne, mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wu Haitao ya yi kira ga kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa wajen tinkarar matsalar fataucin mata da yara mata a lokacin da rikici ya barke.

A wannan rana, kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taron yaki da fataucin mutane a yayin faruwar rikici, inda Wu Haitao ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fama da rikice-rikice a yankuna,inda masu tada rikici su kan samu kudi ta hanyar fataucin mutane, da fakewa da yaki wajen cin zarafin mata, don haka mata da yara mata sun fi fuskantar barazana a fannonin tsaro da kiwon lafiya da mutumci.

Wu Haitao ya ce, batun fataucin mata da yara a yayin faruwar rikici yana shafar kasashe da dama kamar kasashen da suka fito, kasashen da aka yada zango da su, da kuma kasashen da aka karbe su. Don haka, ya kamata kasashen da abin ya shafa da hukumomin kasa da kasa su hada kai don kawo karshen wannan matsala.

Wu Haitao ya kara da cewa, Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da kasa da kasa don samar da zaman lafiya da tsaro, da kare hakkin mata da yara mata, da kawar da cin zarafin mata a yayin rikici, da yadda ake sayar da mutane musamman mata da yara mata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China