A jiya Alhamis 9 ga wata, hukumar lafiya ta duniya WHO ta ba da sanarwar cewa, ya zuwa yanzu an kawo karshen cutar Ebola da ta barke a Liberiya. Wannan shi ne karo na hudu da ba a samu karin mutanen da suka kamu da cutar Ebola cikin kwanaki 42 tun bayan bullar cutar a kasar a cikin shekaru biyu da suka wuce a kasar ta Liberiya.
Kawo yanzu, an shiga matakin kara sa ido kan Liberiya na tsawon kwanaki 90. Da zarar an sami wani mutum da ya kamu da cutar, hukumar da ke hada yaduwar cutar za ta killace shi daga sauran jama'a nan take.(Fatima)