Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar a ranar Talatar da ta gabata cewar, babu bukatar kafa cibiyoyin ba da kulawar gaggawa ga masu cutar Ebola wato PHEIC a kasashen yammacin Afrika.
Matakin na WHO ya biyo bayan wani taro ne da kwamitin ba da kulawar gaggawa na cutar Ebola, karkashin kulawar dokokin kasa da kasa game da yaki da cutar Ebola a yammacin Afrika, wanda aka gudanar a jiya Talata.
WHO ta lura cewar, kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo, sun cika ka'idojin hukumar lafiya wajen kawar da cutar ta Ebola, bayan gwajin da aka gudanar na ware kwanaki 42 da karin kwanaki 90 ba tare da samun bullar cutar ba.
WHO ta ce, a yanzu haka babu kwayoyin cutar ta Ebola a yammacin Afrika, ko kuma wata barazana game da barkewar cutar, kuma a halin yanzu dukkanin kasashen na da karfin tunkarar cutar ko da za'a iya samun bullar ta a nan gaba.
Hukumar lafiya ta duniya ta nemi a janye duk wani takunkumin hana zirga zirga da huldar kasuwanci a kasashen na Guinea, da Liberia da kuma Saliyo wanda aka sanya tun bayan samun bullar kwayar cutar wacce ta hallaka mutane sama da dubu 11, wasu 28,600 kuma suka yi jinya a shekarar 2013.(Ahmed Fagam)