WHO ta bada umurnin gudanar da wani kamfen allura a Guinee bisa fargabar sake barkewar Ebola
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta umurci wani kamfen allura a kasar Guinee inda aka gano wasu mutane takwas dake dauke da cutar Ebola wadanda daga cikinsu bakwai suka mutu tun cikin karshen watan Febrairu lamarin da ya janyo fargaba game da yiwuwar sake barkewar wannan cuta a kasar, a cewar wata sanarwar cibiyar kungiyar da aka fitar a ranar Jumm'a. Sanarwar ta ce, daruruwan mutane da ake fargabar sun yi mu'amala tare da wadannan marasa lafiya takwas da suka kamu da cutar Ebola a yankunan Nzerekore da Macenta, dake kudancin Guinee, sun samu wata allurar gwaji domin dakile barkewar cutar ta baya bayan nan a cikin kasar. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku