in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kawo karshen cutar Ebola a Saliyo
2016-03-18 11:29:04 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce yanzu haka babu sauran wani mutum ko da guda dake dauke da cutar Ebola a kasar Saliyo. Hakan dai ya biyo bayan shafe kwanaki 42 da aka yi, ba a samu karin wani da ya kamuwa da cutar ba.

Wata sanarwa da aka yada ta kafofin watsa labaran kasar, ta rawaito ministan kiwon lafiyar kasa Dr. Abu Bakarr Fofanah, na godewa daukacin al'ummar Saliyo, a madadin shugaban kasar Ernest Bai Koroma, bisa hadin kan da suka bayar har aka kai ga shawo kan cutar baki daya. Dr. Fofanah ya kara da cewa, tun bullar cutar a karon farko cikin shekarar 1976 a Zaire, an sake samun bullar ta har karo 40 a sassan duniya daban daban, inda ta bulla karo 35 a kasashen Afirka

Daga nan sai ya bayyana bukatar ci gaba da sanya ido, da daukar matakan kandagarki, domin wanzar da nasarar da aka cimma a halin yanzu, tare da kaucewa sake bullar cutar a nan gaba.

Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakanin jami'an WHO da ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta Saliyo, jami'an sun bayyana nasarar da aka samu a matsayin wani muhimmin mataki, a yakin da kasar ta fafata da cutar ta Ebola. A daya bangaren kuwa, WHO ta jinjinawa gwamnatin Saliyo, da wadanda suka goya mata baya, da ma sauran al'ummar kasar bisa jajircewarsu wajen ganin bayan cutar ta Ebola.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China