in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chukwueze na shirin bugawa FC Porto tamaula
2016-06-07 11:11:42 cri
Alamu na nuna cewa dan wasan gaban kungiyar kwallon kafar Najeriya ajin matasa wato Flying Eagles Samuel Chukwueze, zai bugawa kungiyar FC Porto ta kasar Portugal kwallo, bayan da shirin komawar sa Arsenal ya gamu da cikas.

A baya dai ana zaton Chukwueze zai bugawa Arsenal din kwallo shi da takwaransa na Flying Eagles din Kelechi Nwakali, kafin daga bisani wannnan shiri ya gamu da matsala.

Wata majiya ta tabbatar da cewa Chukwueze ya samu gayyata daga Porto, kuma abun da kawai ya rage shi ne kammala wasannin share fagen gasar AFCON ta 'yan kasa da shekaru 20 suke bugawa. Majiyar ta ce da zarar an kammala hakan, dan wasan zai isa FC Porto domin fara wasa.

A baya dai dan wasan ya shirya bugawa Red Bull Salzburg wasa, kafin wannan shiri ya hadu da cikas. Dan wasan dai na haskawa matuka a fannin tamaula, inda tuni ya ciwa kungiyar ta Fyling Eagles kwallaye a wasannin sada zumunta biyu da suka buga.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China