in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Siasia: Yawan kura-kurai ya janyo mana rashin nasara
2016-06-06 14:34:13 cri
Kocin kungiyar kwallon kafar Najeriya 'yan kasa da shekaru 23 wadda ake wa lakabi da "Dream Team" Samson Siasia, ya ce kura-kurai da 'yan wasan sa suka rika yi tun daga take kwallo har zuwa karshen wasan su da Denmark ne ya janyo masu kwasar rashin nasara.

Siasia wanda ya bayyana hakan bayan da kasar Denmark ta doke Dream Team din da ci 6 da biyu, a wasan da suka buga ranar Asabar, ya ce tun da yake horas da 'yan wasa ba a taba doke kungiyar sa da ci 6 ba. Dream Team na Najeriya dai sun buga wasa ne da takwarar su ta kasar Denmark a filin wasan Goyang na kasar Koriya ta Kudu, a ci gaba da buga gasar Suwon da ake yi.

Siasia ya ce 'yan wasan sa sun yi sakaci wajen tsaron gida kana 'yan wasan gaba suka kasa cin kwallaye bayan samun damammaki masu yawa. Duk dai da hakan kocin ya ce wasan da suka bugawa ya ba su damar sake duba na tsakani ga kungiyar domin zaben 'yan wasan da za su wakilci kasar a gasar Olympics dake tafe.

Kafin wasan ta da Denmark, kungiyar Dream Team ta Najeriyar ta fara da rashin nasara ne a wasan ta da koriya ta Kudu, inda Koriyan ta jefa mata kwallo daya mai ban haushi, a wasan da suka buga ranar Alhamis.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China