An yi shawarwari karo na shida a fannin tsaro bisa manyan tsare tsare tsakanin Sin da Amurka a birnin Beijing
A yau Lahadi 5 ga wata, mataimakin ministan harkokin waje na Sin, Zhang Yesui da mataimakin sakataren harkokin waje na Amurka, Antony Blinken sun jagoranci shawarwari karo na shida a fannin tsaro bisa manyan tsare tsare tsakanin Sin da Amurka a birnin Beijing, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi kan muhimman batutuwan da suka fi jawo hankulansu, kamar tsaron ikon mallakar kasa, da dangantaka tsakanin rundunonin sojan kasashen biyu, da tsaron yankin teku, da tsaron yanar gizo, da tsaron sararin sama da sauransu.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku