A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a matsayin kasashen 2 na babbar kasa mai tasowa da kuma babbar kasa mai ci gaba, kana manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, ya kamata Sin da Amurka su yi kokarin kulla dangantakar manyan kasashe a tsakaninsu ta yadda jama'ar kasashen biyu har ma daukacin al'ummar duniya za su amfana.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, shekarar bana ita ce shekarar farko ta aiwatar da shirin raya kasar ta Sin na shekaru biyar biyar karo na 13,kuma an yi imanin cimma burin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin. A nan gaba Sin za ta kara samar da dama don yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya ciki har da kasar Amurka. (Zainab)