in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Andy Murray ya doke Novak Djokovic a gasar tanis ta Italiya
2016-05-19 09:22:55 cri

Dan wasan tanis daga Birtaniya Andy Murray, ya lashe gasar tanis ta kasar Italiya, bayan da ya doke Novak Djokovic da ci 6 da 3, da kuma 6 da 3.

Wannan ne dai karo na farko da Andy Murray ya samu nasara kan Djokovic cikin karawa 5 da 'yan wasan suka yi. Ana kallon wannan nasara ta Murray tamkar kyauta ce ya yiwa kan sa, a gabar da yake bikin cika shekaru 29 da haihuwa.

Yanzu haka dai Murray zai haye matsayi na biyu a ajin bajimta, gabanin bude gasar tanis ta kasar Faransa da za a fara ranar 22 ga watan nan na Mayu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China