in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Za a bude sansanin horaswa na 'yan wasan kokawa gabanin fara gasar Olympics
2016-05-19 09:22:02 cri

Hukuma mai kula da wasan kokawa ta kasar Najeriya, ta sanar da cewa za ta bude sansanin horas da 'yan wasan kokawa cikin wannan mako domin amfanar 'yan wasan kokawar kasar 7, wadanda za su halarci wasannin Olympics a kasar Brazil.

Shugaban hukumar wasan kokawa ta Najeriya Daniel Igali, shi ne ya gaya wa manema labaru hakan a jihar Legas, yana mai cewa an tsai da kudurin hakan ne, ganin yadda ma'aikatar harkokokin wasannin kasar ta yi jinkirin kaddamar da horaswa ga 'yan wasan da za su halarci gasar ta Olympics.

Jami'in ya ce hukumarsa ba za ta ci gaba da jira ba, ganin cewa za a fara wasan a watan Agusta, amma har yanzu ba a fara horar da 'yan wasan kasar ba.

'Yan wasan da za su shiga sansanin horaswa da hukumar ta kafa sun hada da maza 2 da mata 5, wadanda suka samu gurbi na halartar wasannin Olympics na wannan karo.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China