in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron shawarwarin Shangri-La karo na 15 a Singapore
2016-06-06 10:22:43 cri

A jiya Lahadi 5 ga wata ne aka kammala babban taron tsaron Asiya wanda aka fi sani da taron shawarwarin Shangri-La a kasar Singapore.

A yayin taron, wakilai da dama sun yi kirayi ga kasa da kasa da su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin cimma moriyar juna.

Mataimakin babban hafsan hafsoshin kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na kasar Sin Sun Jianguo, ya gabatar da jawabi a yayin bikin rufe taron, inda ya bayyana cewa, kasar Sin na dukufa wajen ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa gaba a wannan fanni, ta yadda za a iya cimma moriyar juna, da kuma kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa da ta dace da bukatun kasa da kasa, da kuma hanyoyin neman bunkasuwar su.

Kaza lika, ya ce, ya kamata kasashen duniya su kara gudanar da shawarwari domin samun fahimtar juna, da kuma cimma matsayi daya kan wasu batutuwa masu alaka da hakan. Ta haka ne a cewarsa za su samu dabaru masu kyau wajen warware sabanin dake tsakanin kasashen da batutuwan suka shafa, yayin da kuma hakan zai ba da damar hana aukuwar rikice-rikice. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China