in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Henry Kissinger: Kasashen Sin da Amurka za su kasance abokan hadin kai maimakon abokan gaba
2016-03-20 13:17:49 cri
Jiya Asabar, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger, wanda ya taba taimakawa kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Amurka ya bayyana cewa, ba za a kasance da Tarkon Thucydides a tsakanin kasashen Sin da Amurka ba, kasashen biyu za su kasance abokan hadin kai ne a nan gaba, ba abokan gaba ba.

Henry Kissinger ya bayyana hakan ne a yayin da yake halartar taron koli game da tatttalin arziki na dandalin tattaunawar bunkasuwar kasar Sin na shekarar 2016, wanda har yanzu ake gudanarwa a nan birnin Beijing. Henry Kissinger ya ce, Tarkon Thucydides na nufin cewa, wata sabuwar kasa mai tasowa za ta yi hammaya har da tayar da yaki da manyan kasashe dake kasancewa a halin yanzu. Ya kara da cewa, kasashen Amurka da Sin su ne kasa ta farko da ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya, wadanda suka samu sakamako mai kyau a wasu fannonin hadin kai. Duk da kasancewar wasu 'yan bambamce bambanci a tsakaninsu, amma dukkansu na da niyyar kawar da su, da kuma neman samu ra'ayin bai daya.

A yayin da yake halartar tattaunawa kan dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka mai taken "Hana shiga Tarkon Thucydides", Henry Kissinger ya jaddada cewa, "zamani na samu bunkasuwa, kuma duniya na samun ci gaba ne", ya kara da cewa, warware rikici tsakanin shiyya-shiyya, da kafa tsarin zaman lafiya hanya ce da ake bi a yanzu haka. Kasashen Sin da Amurka na kokari don cimma wannan buri.

Kan makomar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka a nan gaba, Henry Kissinger ya jaddada cewa, kamata ya yi a nuna basira kan wannan batu, yana mai fatan kasashen biyu za su kasance abokan hadin kai, maimakon abokan gaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China