An gudanar da taron tattaunawa kan kiyaye tsaro bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Amurka a birnin Washington
A jiya Alhamis ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Yesui, da mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, suka shugabanci taron tattaunawa kan kiyaye tsaro bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Amurka a birnin Washington na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan batun kiyaye tsaro bisa manyan tsare-tsare.
Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da yin amfani da tsarin tattaunawa don kiyaye tsaro bisa manyan tsare-tsare a kasashen su, da inganta mu'amala, da hadin gwiwa, da warware matsalolin dake tsakaninsu, da kuma sa kaimi ga bunkasa dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata. (Zainab)