Wani jami'in kan iyaka ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa masunta sun tabbatar shigowar 'yan sandan Uganda a cikin RD-Congo.
Wadannan 'yan sandan Uganda sun gudanar da kama jiragen ruwan kamun kifi na Congo, a cewar wannan majiya.
Zuwan rundunar sojojin ruwan Congo, ya janyo musanyar wuta tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ya hadasa mutuwar dukkan 'yan sandan hudu da jikkatar soji daga bangaren RDC, in ji Olivier Umaka, wani jami'in ma'aikatar muhalli dake kan iyaka da tafkin Albert. An isar da gawawwakin 'yan sandan Uganda a Bunia, wani yankin dake yammacin tafkin Albert.
An dai fara tuntubar juna tsakanin hukumomin Uganda da RD-Congo, kan wannan lamari, ko da yake har yanzu kasashen biyu ba su yi wata sanarwa ba. (Maman Ada)