Gangamin na da nufin karfafa tattaunawa a bainal jama'a a kan batutuwan da suka shafi wariyar launin fata ta inda za'a aiwatar da shirye shirye da dama, in ji wadanda suka shirya bukin.
Gidauniyoyin Nelson Mandela da Ahmed Kathrada su ne suka shirya gangami cikin hadin gwiwwa da a kalla sauran kungiyoyi 80 karkashin shirin hana wariyar launin fata a Afrika ta kudu.
Wadanda suka shirya gangamin sun bukaci al'ummar kasar ta Afrika ta kudu da su gano, fadakar tare da aiwatar da shiri mai kyau da dabaru da zai hana wariyar launin fata da rage tare da magance wariyar launin fata baki daya, a kuma fatan al'ummomin kasar su yi cudanya su kuma dauki mataki na kalubalantar duk wani nau'in wariyar launin fata a kuma gyara shi inda ya auku. (Fatimah Jibril)