in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Zuma: ba za a amince da hambarar da gwamnati ta hanyar nuna karfin tuwo ba
2016-05-02 12:29:30 cri
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu, ya bayyana cewa ko alama ba za a amince da duk wani matakai na amfani da harzuka jama'a ko nuna karfin tuwo, da nufin gurgunta yanayin zaman lafiya da zaman karko a Afirka ta Kudu ba. Kalaman na shugaba Zuma dai sun biyo bayan wasu zantuka na rade-radin yiwuwar hambarar da gwamnatin kasar mai ci ta hanyar nuna karfin tuwo.

Jacob Zuma wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a gun taron bikin ranar kwadago ta duniya a jiya Lahadi a birnin Pretoria, ya kuma kara da cewa, wasu rukunin al'ummar kasar na da nufin tayar da zaune tsaye, da yada ra'ayoyi marasa tushe, da kuma neman kawo baraka tsakanin al'ummar kasar, don haka ya zama wajibi jama'ar kasar su yi taka tsan tsan da wannan lamari. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China