in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu kyawawan sakamako ta fuskar diflomasiyya a bana
2014-12-12 15:34:39 cri
A yayin liyafar murnar shigowar sabuwar shekara da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya a jiya Alhamis 11 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, a shekarar 2014, kasar Sin ta samu ci gaba, da sakamako mai yawa ta fuskar harkokin diflomasiyya. A bana, kasar Sin ta himmatu wajen raya abokantaka a duk duniya, har ma ta cimma nasarar kulla dangantakar abokantaka tare da kasashe 67 da kuma kungiyoyin shiyya-shiyya guda 5. Hakan ya shaida ra'ayinta na kulla dangantakar abokantaka a maimakon kulla kawance a fannin diflomasiyya.

Wang Yi ya ce, kasar Sin na mai da hankali kan yunkurin neman samun bunkasuwa tare da kasashen da ke yankin Asiya da Turai. Don haka ta fidda shirin zirin tattalin arziki na siliki, da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21 bisa aniyar koyi da juna da fahimtar juna, gami da zama cikin yanayi na lumana, wanda kawo yanzu dai ya riga ya samu amincewar kasashe har guda 50 da ke kan hanyar.

Haka zalika, Wang Yi ya ce, a bana, kasar Sin ta samu nasarar shirya manyan taruruka biyu, da suka hada da babban taron inganta hadin gwiwa da fahimta tsakanin kasashen yankin Asiya, da kuma kwarya-kwaryar taron shugabanni mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifi ta APEC, inda ta ba da gudumawa ta musamman, kan kiyaye zaman lafiya da zaman karkon yankin, da kuma kara azama ga hadin gwiwa da bunkasuwarsu.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma ba da taimako yadda ya kamata wajen warware matsalar nukiliyar kasar Iran, da rikicin zirin Korea da na kasar Ukraine da na Falesdinu da Isra'ila, kana da yakin basasa na kasar Sudan ta Kudu. Ta kuma mai da hankali sosai wajen yaki da ta'addanci da kuma cutar Ebola, bisa ka'idojin nuna adalci, da kuma inganta shawarwarin zaman lafiya. Hakan ya sa ta ba da samar da moriya a fannin kiyaye zaman lafiya da lumana tsakanin kasa da kasa, da shiyya-shiyya, bisa matsayinta na kasa mai kokarin sauke nauyin dake wuyanta.

Sa'an nan shekarar 2015 mai zuwa, za ta kasance wata muhimmiyar shekara mai ma'ana ga kasar Sin, da ma daukacin duniya baki daya. Dalilin da ya sa haka kuwa shi ne, sabo da a shekarar ta badi, kasar Sin za ta shirya gagarumin biki na cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da hare-haren Japanawa, baya ga ci gaba da shirinta na zurfafa yin kwaskwarima a gida daga dukkan fannoni, da kuma tafiyar da harkokin kasar bisa doka.

A cewar Wang Yi, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da gamayyar kasashen duniya, wajen kiyaye adalci da tsarin zaman lafiya da aka samu bayan yakin duniya. Bugu da kari, za ta gaggauta aikin tsara shirin neman bunkasuwa bayan shekarar 2015, wanda zai shafi muradun duniya baki daya, musamman ma na kasashe masu tasowa, a kokarin ba da sabuwar gudumawa ga rayuwar daukacin ci gaban bil Adama baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China