Bayan wani taron ministoci a fadar shugaban kasar Guinea a ranar Alhamis, shugaban kasar Alpha Conde ya bukaci gwamnatin kasar da ta karfafa kokarin ma'aikatar dake kula da harkokin jama'a domin yaki da fyade, auren dole da kuma kaciya.
Shugaba Alpha Conde ya jaddada muhimmancin taimakon kungiyoyin addinai, da kuma hukunce hukuncen ladabtarwa da ya kamata a yanke kan wadanda suka aikata wadannan ayyuka, in ji kakakin gwamnatin Guinea Albert Damantang Camara.
Shugaban Guinea ya bayyana damuwarsa game da cin zarafin da aka yi wa mata, wanda ya hada da fyade, auren dole da kaciya. Inda a yayin wani taron karawa juna sani da shugabannin addinin musulunci suka shirya baya bayan nan, shugaban kasar ya bukaci shugabannin da su dauki wadannan matsalolin da mata suke fuskanta da muhimmanci. Musammun ma abin da ya shafi auren dole da ya zama ruwan dare a kasar, inda kananan 'yan mata masu shekaru 13 da aifuwa ko kasa ake ba da su aure ga mazan da suka lunka shekarunsu har sau uku.
Game da kaciyar 'yan mata, Guinea na daga cikin manyan kasashe uku na Afrika inda ake gudanar da wannan muguwar al'ada. Gwamnatin kasar ta yi alkawarin kara rubunya kokari domin yaki da wannan annoba, dake jawo illa ga lafiyar 'yan mata da matsalar ta fi shafa, in ji kwararru. (Maman Ada)