Cikin wata sanarwar da ofishin ta ya fitar, uwargida Zuma, ta jinjinawa nadin sabbin ministocin gwamnatin rikon kwarayar kasar da shugaba Salva Kiir Mayardit ya yi, bisa tanajin yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da aka cimma a bara. Ta ce daukar wannan mataki zai taimaka matuka wajen shawo kan matsalolin dake addabar kasar.
Zuma ta kara da cewa tashe tashen hankula da suka rika faruwa cikin kusan shekaru biyu da rabi a Sudan ta Kudu, sun haddasa gagarumin koma baya ga tattalin arzikin kasar, tare da gurgunta zamantakewa da tsarin siyasar kasar, matakin da ya kai ga fadawar al'ummar ta cikin tsananin bukatar tallafin jin kai. (Saminu Alhassan)