in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta fara ba da fasfon Afrika
2016-05-08 12:22:30 cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta fara ba da fasfon nahiyar, in ji ministar harkokin waje da kasuwancin kasa da kasa ta kasar Kenya, madam Amina Mohamed, a yayin wani taron manema labarai a ranar Asabar a birnin Nairobi. Ministocin harkokin waje sun fara cika takardu da ka'idoji domin fasfunan Afrika da za a bayar a yayin taron kungiyar AU a cikin watan Yuli mai zuwa, in ji madam Mohamed. Ina farin ciki na sanar da ku kamar yadda makakan da shugabannin kasashe da gwamnatoci na AU suka tanada domin kawo sassauci ga zirga zirga cikin 'yanci a nahiyar, ta hanyar kafa wani fasfon Afrika domin shugabannin kasashe da ministoci. Wannan tsari na ba da fasfon ya fara tun ranar Jumma'a, in ji madam Mohamed a dabra da taron kwamitin zartaswa na kungiyar AU karo na hudu. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China