in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta koka kan tafiyar hawainiyar hadewar nahiyar
2016-05-30 13:43:02 cri
Kungiyar tarayyar Afirka wato AU, ta koka matuka game da tafiyar hawainiyar da ake samu a kokarin da ake yi na dunkelewar nahiyar waje guda.

Mataimakin kwamishina a hukumar zartarwar kungiyar AU Erastus Mwencha ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin Kenya cewa,babbar matsalar da ke kawo cikas ga wannan kokari, ita ce fargabar da wasu kasashen nahiyar ke yi cewa, ba za su amfana ba idan har nahiyar ta zama kasuwar bai daya.

A saboda haka jami'in kungiytar ya ce kamata ya yi masu bincike su fito da wasu muhimman alkaluma da za su nuna cewa, nahiyar za ta ci gajiyar wannan manufa maimakon su rika nuna dari-dari.

Mwencha ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi yayin taron karawa juna sani na kwanaki 5 na dandalin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka(AERC).

Ya kuma bayyana cewa, siyasar tattalin arziki ita ce ta ke kawo nakasu wajen hanzarta aiwatar da shirin hadewar yankin waje guda. Wannan ya sa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar ta tsaya a kashi 12 cikin 100, yayin da a wasu shiyyoyin ta kai kusan kashi 50 cikin 100.

Jami'in hukumar ta AU ya kuma ce, idan har aka dunkule tattalin arzikin nahiyar waje guda, wasu kasashen za su yi asara a wasu sassa kana su amfana a wasu, koda ya ke hakan ya dogara da irin takarar da suke yi.

Sama da masu bincike,malaman jami'o'i da masu tsara manufofi 200 ne ke halartar wannan taro.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China