AU ta yi allawadai da karuwar matsayin cin hanci a Afrika
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi allawadai a ranar Asabar da karuwar matsayin cin hanci a nahiyar Afrika. Da take magana a gaban manema labaru a birnin Nairobi a dabra da taron kwamitin zartaswa na AU, shugabar kwamitin tarayyar AU, madam Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana gaban 'yan jaridar cewa cin hanci na lalata yardar al'ummomi kan gwamnatocinsu. Wannan na lalata albarkatun gwamnati da suka dace domin samar da muhimman ayyuka ga jama'a kamar ilimi da kiwon lafiya, in ji madam Dlamini-Zuma. Haka kuma ta bayyana cewa cin hanci a wani bangare da wasu tabi'u dake gudana a nahiyar Afrika. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku