in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fidda bayani game da matsayin gwamnatin Sin kan karar da Philippines ta gabatar
2014-12-07 17:45:31 cri
A Lahadin nan ne aka ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta fidda wani bayani, dake kunshe da matsayin gwamnatin kasar Sin, kan batun karar da kasar Philippines ta shigar gaban kuliya, ta na mai bukatar sulhunta batun ikon yankin tekun kudu, batun da Philippines din da Sin ke takaddama a kan sa.

Kasar Sin dai ta nanata cewa, ba za ta yarda ta shiga wannan batu na sulhu ba, kan kotun da aka gabatarwa karar, ba ta da ikon sauraron korafin bisa dokokin da suka shafi dukkan fannoni.

A ranar 22 ga watan Janairun bara ne dai Philippines ta gabatar da karar sulhun kan batun yankin tekun kudun cin ta da Sin. Daga bisani kuma ta yi watsi da rashin amincewar da Sin ta nuna game da batun, tare da yunkurin tabbatar da ra'ayin kashin-kanta na sulhu.

Sai dai matsayar kasar ta Sin ta tabbatar da cewa, Philippines ta gabatar da koke ga kotu ne kan batun da ya shafi ikon mallakar cikakken yankin kasa, na wasu tsibirai dake yankin tekun kudancin tau, wanda ya zarce hurumin yarjejeniyar dokar yankin teku ta MDD, wanda kuma ya sa kotun ta sulhu ba ta da ikon sauraron wannan batu.

Dadin dadawa, bayanin ya kara da cewa, daidaita batun yankin tekun na kudu ta hanyar shawarwari, ita ce dabara da kasashen biyu suka cimma bisa ra'ayoyin su, da kuma ayyukan da suke gudanarwa a yankin tekun na kudu. Aikin da Philippines din ta keta dokokin dake da alaka da shi.

Bugu da kari bayanin ya kara da cewa, batun yankin teku na kudu ya shafi kasashe da dama, kuma kamata ya yi a yi kokarin warware shi ta hanyar hakuri da hikimar bangarori daban daban. Kana kasashen da abin ya shafa su girmama tarihi da dokokin duniya, su kuma warware batun ta hanyar yin shawarwari yadda ya kamata. Kafin hakan kuma, kamata ya yi bangarori daban daban su gudanar da shawarwari, a yi kokarin yin hadin gwiwa, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki na teku, su kuma kara amincewa da juna, da zummar samar da yanayi mai kyau wajen warware wannan batu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China