in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda ya dauki alwashin yaki da cin hanci
2016-06-01 10:14:40 cri
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya dauki alwashi a ranar Talata na farautar dukkan manyan jami'an gwamnati da cin hanci ya wa katutu, a yayin bikin kama sabon wa'adin aikinsa na shekaru biyar masu zuwa, ya jaddada cewa wannan annoba tana jinkirtar da cigaban tattalin arzikin kasa.

A cikin jawabinsa na farko kan halin da kasa take ciki tun lokacin rantsar da shi kan sabon wa'adinsa a ranar 12 ga watan Mayu, mista Museveni ya bayyana a ranar talata cewa zai yaki cin hanci kamar yadda ya kawar da rashin da'a a cikin rundunar sojojin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China