A yayin ganawarsu, Yan Junqi ta bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar Uganda wajen neman hanyar raya kasa da kanta, domin bunkasa tattalin arzikin kasar, yayin da kuma ake kyautata zaman rayuwar al'ummomin kasar, haka kuma, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Uganda wajen aiwatar da batutuwan da shugabannin kasashen biyu suka cimma ra'ayi daya wajen yin hadin gwiwa, ta yadda za a iya kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu har zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangaren kuma, shugaba Museveni ya ce, kasarsa tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, musamman ma a fannin habaka ayyukan masana'antu da ayyukan noma da dai sauransu, domin ba da tallafi da al'ummomin kasashen biyu. (Maryam)