in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda Museveni ya yi ratsuwar kama aiki
2016-05-13 10:28:40 cri
A ranar 12 ga wata, shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi rantsuwar kama aiki a birnin Kampala hedkwatar kasar, don fara wa'adin aiki na daban na shekaru 5.

Shugabannin kasashen Afrika 14 da sauran ragowar shugabannin kasashen duniya sun halarci bikin. A cikin jawabin da Museveni ya gabatar a yayin bikin, ya bayyana cewa, zai yi kokari don tabbatar da mulkin kan kasar. Yana mai cewa, ya zama dole wasu kasashe su daina yin katsalanda game da yadda kasashen Afrika suke tafiyar da harkokinsu.

Museveni ya ce, zai dukufa ka'in da na'in wajen yaki da cin hanci da rashawa, da raya zirga-zirga da makamashi, da ababen more rayuwa, don sanya kasar Uganda cikin kasashen da ke da kudin shiga fiye da rabin kasashen daban daban a duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China