Gamayyar masu zuba jari daga kasar Sin ne zasu dauki nauyin biyan kudaden aikin wanda ke karkashin kulawar gwamnatocin Sin da Uganda.
Bikin fara aikin, ya samu halartar shugaban kasar Yoweri Museveni, da mataimakinsa Edward Ssekandi, da kusoshin gwamnatin kasar tare da tawagar masu zuba jari na kasar Sin.
shugaba Museveni, ya bayyana cewar idan aikin ya kammala za'a samu bunkasuwa, sannan manoman kasar zasu samu Karin kudaden shigar su.
Da ma dai gwamnatin kasar tana gudanar da wasu ayyuka na giggina masana'antu da nufin farfado da ci gaban tattalin arzikin kasar.
Masu zuba jarin na kasar Sin sun bayyana cewar, kamfanin zai fi maida hankali ne wajen samarwa da kuma sarrafa kayyayakin amfanin gona da kiwon kaji da na dabbobi domin biyan muradun jama'ar kasar da jama'ar kasashen dake dab da ita.
Aikin zai samar da guraben aikin yi kimanin 25,000 da kuma samar da kwarewa ga jama'ar kasar.
Kafin bikin kaddamar da aikin, masu zuba jarin da gwamnatin Uganda sun rattaba hannu kan yarjejeniya game da bunkasa aikin gona a kasar.(Ahmad Fagam)