in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 49 sun rasu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a Kenya
2016-05-08 13:15:52 cri
Bisa labarin da hukumar kula da harkokin bala'u ta kasar Kenya ta fidda, an ce, tun ranar 29 ga watan Afrilu zuwa ranar 7 ga watan da muke ciki, ana yi ta ruwan sama kamar da bakin kwarya a babban birnin kasar Kenya, Nairobi, lamarin da ya haddasa rushewar gidaje da wasu hadarurrukan da suka haddasa rasuwar mutane guda 49, yayin da kimanin mutane 50 aka rasa inda suke a halin yanzu.

Haka kuma, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta yi a birnin Nairobi, wani gini mai bene shida dake yankin Huruma a gabashin birnin Nairobi ya rushe a ran 29 ga watan Afrilu, lamarin da ya haddasa rasuwa da jikkatar mutane da dama, ban da haka kuma, ana ci gaba da samun wasu hadarurruka a sauran yankunan dake birnin Nairobi sakamakon wannan bala'i.

Kana, bisa labarin da aka samu, an ce, hukumomin da abin ya shafa na kasar Kenya sun riga sun rushe wasu gidajen da mai iyuwa ne za su yi rushewa ba zato ba tsammani sakamakon bala'in, domin kawar da sake faruwar iri wannan hadari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China