in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Rasha da sakataren harkokin wajen Amurka sun yi shawarwari ta wayar tarho kan yanayin da ake ciki a Syria
2016-05-30 11:28:26 cri
A jiya Lahadi ne, ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Viktorovich Lavrov ya zanta ta waya da takwaransa na Amurka, John Forbes Kerry, inda suka yi shawarwari kan yanayin da ake ciki a Syria da sauransu.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ba da sanarwar cewa, jami'an harkokin wajen kasashen biyu sun ci gaba da yin shawarwari kan yanayin da ake ciki a Syria, da shawarar da Rasha ta bayar ta daukar matakan da suka dace kan kungiyoyin 'yan ta'addada da kungiyoyin da ke dauke da makamai ba bisa doka ba da ba su martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma.

Sanarwar ta kara da cewa, a yayin shawarwari, ministocin biyu sun tabo batun Ukraine, da wasu batutuwan dake shafar dangantakar kasashen biyu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China