Wang Yi ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 70 da kasa da kasa suka cimma nasarar yaki da 'yan Fascist da kuma yadda kasar Sin ta cimma nasarar yaki da hare-haren da sojojin maharan Japan. A cikin shekaru 70 da suka gabata, a yayin da kasar Sin ta yi kokarin bunkasa kanta, da ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a duniya da kuma kare da kyautata tsarin kasa da kasa bayan yakin da kuma kiyaye odar kasa da kasa a duniya.
Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce ta farko da ta sa hannu kan kundin tsarin mulkin dokokin MDD, kuma manufofin harkokin waje na kasar Sin suna bin ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD. A matsayin kasata na mamba ta dindindin ta kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ta jefa kowace kuri'a don tabbatar da adalci a tsakanin kasa da kasa da kuma moriyar kasashe maso tasowa da kasashe kanana masu rashin samun karfi. Kana kasar Sin ta jefa kowace kuri'a ta nuna kiyayya rashin amincewa don kawo cikas gahana ayyukan tada yaki da kama karya a duniya.
Haka zalika kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta shiga yi kokarin ba da taimakonta wajenayyukan warware manyan matsalolin duniya, da inda ta kafa tsarin shawarwari a tsakanin bangarori shida don kawar da tattauna batun makamashin nukiliya a zirin Koriya, kana ta sa kaimi ga yin shawarwari ta hanyar siyasa kan batun nukiliya na Iran, batun Ukraine, da na yankin gabas ta tsakiya da kuma na , Sudan ta Kudu da dai sauransuwadanda ke janyo hankalin duniya. A kowace rana, masu ma'aikatan kiyaye zaman lafiya daga kasar Sin fiye da dubu 3 suna gudanar da ayyukansa ayyukansu a wurare daban daban na duniya, ya zuwa yanzu an tura jiragen ruwa har sau 59 zuwa mashigin tekun Aden, tekun Somaliya don, wadanda suka bada kariya ga jiragen ruwa na Sin da kasashen waje kimanin dubu 6. (Zainab)