A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro domin tattaunawa kan yaki da dakarun kungiyoyin ta'addanci da suka fito daga kasashen ketare. A yayin da yake jawabi, Liu Jieyi ya ce, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta dauki matakai yadda ya kamata domin hana yaduwar bidiyoyi da kuma ra'ayoyin 'yan ta'adda ta hanyoyin zamani, da kuma lalata shirinsu na shigar da mambobi, neman kudade da kuma shirya aikace-aikaken ta'addanci.
Kaza lika, ya kamata gwamnatocin kasa da kasa su gudanar da kudurorin babban taro da kwamitin tsaron MDD da abin ya shafa yadda ya kamata, domin karfafa aikin sa ido kan harkokin intanet.
Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da kudurin kwamitin sulhu na MDD yadda ya kamata, da kuma karfafa aikin yaki da ta'addanci bisa dokokin da abin ya shafa. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwar yaki da ta'addanci dake tsakanin kasa da kasa da shiyya-shiyya, da kuma samar wa kasashe masu tasowa kayayyakin yaki da ta'addanci da kuma ba su horaswa kan aikin yadda ya kamata. (Maryam)