in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan manufar Sin ta fita waje za ta amfani jama'ar Sin da ma na kasashen duniya baki daya, in ji masanin MDD
2015-07-07 11:07:43 cri
Masani mai kula da tasirin da bashi ke kawowa kiyaye hakkin dan Adam, a majalisar kula da harkokin kare hakkin dan Adam ta MDD Juan Pablo Bohoslavsky, ya ce yana fatan manufar Sin ta fitar kamfanonin ta da sana'oi zuwa ketare, za ta haifar da moriya ga gwamnatoci, da kamfanonin kasa da kasa, tare da riba ga jama'ar kasar Sin, da na kasashen duniya baki daya.

Bohoslavsky ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin ziyarar aiki da yake gudanarwa a nan birnin Beijing.

Ya ce a matsayin ta na sabon tattalin arziki dake samun ci gaba sama da sauran kasashe, kasar Sin ta riga ta samar da tallafi ta kyauta, da ba da rancen kudi mai rangwame ga kasashe fiye da 120. Bayan da aka fara aiwatar da manufar fita waje, kamfanonin Sin sun taimakawa kasashe masu tasowa da dama, wajen gina hanyoyin jiragen kasa, da na motoci, da harkokin sadarwa da sauran ayyukan more rayuwa, wadanda ke sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasashen.

Kana kasar Sin ta gabatar da kiran aiwatar da manufar "Ziri daya da hanya daya", wanda kasashe da dama suka amsa. Bohoslavsky ya ce, wannan manufa za ta kasance mai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, da kara samar da guraben ayyukan yi, da kara samun izinin shiga kasuwanni, da samun moriyar tattalin arziki da ta zamantakewar al'umma.

Haka zalika kuma, Bohoslavsky ya ce rancen kudi da fasahohin da Sin ta samar a fannonin gina ababen more rayuwa, da kiwon lafiya, da aikin gona da dai sauransu, sun bada gudummawa ga kasashe da dama wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma al'adu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China