in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a girmama juna a fannonin al'adu da addinai
2015-04-22 11:16:32 cri

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wang Min, ya ce ana bukatar sa kaimi ga girmama juna a fannonin al'adu, da addinai da kara yin mu'amala da juna, don kafa zamantakewar al'umma ciki zaman lafiya da lumana a fadin duniya baki daya.

Mr. Wang wanda ya bayyana hakan a gun muhawarar da babban taron MDD ya gudanar a jiya Talata, ya ce matsalar talauci na daya daga cikin manyan dalilan dake haifar da tsattsauran ra'ayi da yaduwar ta'addanci a sassan duniya baki daya. Ya ce yaduwar tsattsauran ra'ayi muhimmin dalili ne da ke haifar da ayyukan ta'addanci da rikice-rikice.

Daga nan sai ya gabatar da shawarar kara kwazo wajen bunkasa tattalin arziki, da kawar da talauci, da kyautata zaman rayuwar jama'a, a matsayin muhimmin mataki na kau da tushen ta'addanci. Mr. Wang ya kara da cewa tsattsauran ra'ayi, da ta'addanci abokan gaba ne na dan Adam, don haka ya kamata kasashen duniya su hada kai wajen yakar wannan matsala. Bai kuma kamata a dauki matsaya biyu kan batun ba, kana bai dace a alakanta ta'addanci da wasu kabilu ko addini ba.

Haka zalika Mr. Wang Min ya ce Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen duniya, game da kokarin sa kaimi ga mu'amala, da hadin gwiwa a tsakanin mabanbantan al'adu da addinai, da kuma yin hadin gwiwa tare da sassan duniya daban daban wajen yaki da ta'addanci, da masu tsattauran ra'ayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China