Kwamitin cigaban shiyyar da kuma yin gyare gyare na jihar Xinjiang na hasashen sake tsugunar da iyalai 7.692, da aka rarraba a cikin kauyuka 463, a cikin tsarin wani alkawarin da ya shafi taimakawa mutane dubu 200 samun sabbin gidajen zama nan da shekarar 2020.
A yayin tsawon shekaru biyar da suka gabata, mutane miliyan 1.74 dake jihar Xinjiang suka fita daga kangin talauci da kuma yawan mutane matalauta ya ragu fiye da rabi domin cimma kashi 15 cikin 100.
Jihar Xinjiang na da burin fitar da mutane miliyan 2.61 da suka yi kaura daga kangin talauci nan da shekarar 2020. (Maman Ada)