Mista Xi, dake kuma sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CCPCC), ya bayyana hakan ne a ranar Jumma'a da yamma, a cikin tsarin wani nazari na gungu, da ya samu halartar mambobin cibiyar siyasa ta CCPCC kan matsala da makomar al'ummar da ta tsufa.
Ya maida hankali kan muhimmancin biyan bukatu na wani babban adadin Sinawan da suka tsufa sosai, da kuma warware matsalolin jama'a.
Tare da mafi yawan mutanen da suka tsufa a duniya, kasar Sin ta kyautata kulawa ga wannan bangare, in ji shugaba Xi. Amma, har yanzu akwai sauran abubuwa da dama da za a yi kuma akwai babban gibi tsakanin gaskiyar halin da ake ciki da kuma jira na jin dadin mutane a lokacin da tsufa ya kama su, a cewar Xi Jinping.
Xi Jinping ya yi kira da a rika nuna halayya mai kyau, domin tsofaffin mutane sun cancanci karbuwa da girmamawa daga bangaren al'ummar kasa, da yadda za su bunkasa darajar kansu da 'yanci. (Maman Ada)